Rahotannin da su ke fitowa daga yankin na Gaza sun ce a cikin harin bayan nan da jiragen yakin h.k. Isra’ila su ka kai wa yankin Gaza, a kalla Palasdinawa uku ne su ka yi shahada. Ma’aikatar kiwon Lafiya ta yankin Gaza ta ce; A wani harin da aka kai wa wata mota a Khanyunus, wasu ‘yan’uwa su biyu Umar Abu Diqqah da Ibrahim Abu Diqqah sun yi shahada, sai kuma Khadharat Abu Diqqah.” Sanarwar ma’aikatar kiwon lafiyar ta kuma ce wasu karin mutane biyar sun jikkata sanadin harin. Shedun ganin ido sun ce jirgin yankin h.k. Isra’ila maras matuki ne ya harba makami mai linzami akan motar da ta ke dauke da farafen hula. Kawo ya zuwa yanzu adadin wadanda su ka yi shahada sanadiyyar hare-haren ta’addancin h.k. ISra’ila sun kai 208 sai kuma wadanda su ka jikkata da su ka kai 1550. ABNA
16 Yuli 2014 - 18:20
Lambar labari: 624559
Sojojin H.K. Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare akan yankin Gaza.